Asiri Ya Tonu: An Samu ‘Yan Sanda Da Hannu A Harin Kurkukun Kuje

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Dubun wasu ’yan sanda ta cika bayan an same su suna waya da ’yan ta’adda da suka tsere daga Gidan Yarin Kuje.

An kama ’yan sandan da ke kula da kes din (IPO) ’yan ta’addan ne bayan an tatsi sautin ganawarsu ta waya inda aka ji suna hada baki da ’yan ta’addar da suka tsere.

“Mutum biyu daga cikin ’yan ta’addan da suka tsere sun kira wani IPO suna wata tattaunawa da alamar hadin baki.

“Yanzu haka ana tsare da su ana bincikar su domin gano irin rawar da suka taka,” inji majiyarmu.

Majiyar ta ce ’yan ta’addar kungiyar ISWAP ne suka kai harin suka kubutar da mambobinsu daga gidan yarin, saboda Gwamnatin Tarayya ta ki amincewa da bukatunsu.

Ta bayyana cewa kungiyar da ta kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ce ta kai wa Kurkukun hari.

Ana zargin kungiyar Ansaru, wadda bangare ne na ISWAP, da kai harin jirgin kasan.

Majiyarmu ta ce kunguyar ta kai hari a gidan yarin ne bayan yunkurinta na amfani da fasinjojin jirgin wajen yin musaya domin gwamnati ta sako ’ya’yan mambobinta kuma mayakanta da ke tsare a Kuje da sauran wurare ya gagara.

“Da suka ga bukatarsu ba za ta biya ba, sai suka kai hari,” da ababen fashewa domin su samun saukin shiga gidan yarin.

Ta ce mayakan aka kubutar din za su fitini Najeriya idan ba a dauki matakin da ya dace ba.

Bayanan da muka samu sun ce bayan jami’an hukumar gidajen yari da ke kula da cibiyar, sauran masu samar da tsaro a wurin sun hada da sojoji da ’yan sanda da SSS da Sibil Difens, saboda irin manyan masu laifi da ke tsare da gidan yarin.

Sai dai kuma hukumomi sun yi watsi da rahoton da aka samu kan yiwuwar harin, abin da ya ba wa maharan damar kutsawa cikin gidan yarin.

“Amma abin takaici shi ne ko’ina akwai baragurbi, saboda haka duk da cewa jami’an tsaro sun samu rahoto, ’yan ta’addar sun yi abin da suke so a cikin tsari, babu kuskure.

Rahoton Jaridar Aminiya

Related posts

Leave a Comment