Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar sanadiyyar tashin hankali da barke a wasu sassan kananan hukumomin Jema’a da Kaura, gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar hana walwala na awa 24 a fa?in kananan hukumomin.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar Litinin a garin Kaduna.
Aruwan ya ce an saka wannan doka ce domin jami’an tsaro su iya shawo kan tashin hankalin da ya ?arke a tsakanin mutanen kananan hukumomin kafin ya ya?u zuwa wasu sassan yankunan dake karkashin kananan hukumomin.
Ya ce da zarar an samu natsuwa da kwanciyan hankali gwamnati za ta sanar da inda aka do sa.
Yayi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankalin su gwamnati da jami’an tsaro na aiki tukuru domin kawo karshen matsalolin rashin tsaro a jihar
