Buhari Zai Ziyarci Legas Yau Talata

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Legas, inda zai duba tare da kaddamar da wasu ayyuka da ake yi a jihar.

A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya fitar ta shafukansa na Facebook da Twitter, ya yada hotunan ayyukan da shugaban zai duba tare da kaddamarwa.

Sanarwar ta ce, shugaban zai kai ziyarar ta aiki ne a yau Talata 22 ga watan Maris.

Wani yankin sanarwar ya bayyana cewa Buhari zai duba ayyukan da ake yi a wata tashar jirgin ruwa da ake yi a jihar ta Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! Ahmad ya ce:

“A Yau ne shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki Legas domin duba aikin da ake yi a tashar jirgin ruwan Lekki Deep Sea. Idan aka kammala aikin tashar ruwan tekun mai fa’idoji da yawa, za ta kasance tashar ruwa mafi zurfi a Najeriya kuma ana hasashen za ta kasance daya daga cikin tashoshin jiragen ruwa na zamani a yammacin Afirka.”

Hakazalika, ya kuma ce, shugaban zai kaddamar da wata tasha da gwamnati ta gina tashar jirgin sama na Murtala Muhammed da ke a birnin na Legas.

Related posts

Leave a Comment