Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi watsi da sunansa da aka saka a ginin wasu ?akunan kwanan ?alibai a Kwalejin fasaha ta Ramat a Maiduguri na gwamnatin jihar.
Zulum ya yi watsi da karamcin ne lokacin da yake ?addamar da ginin da ma’aikatar ilimi ta gyara.
A sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar, Zulum ya ce “Ba zan yarda a saka sunana a wani aikin gwamnati ba, a lokacin da nake kan mulki. Ya kamata ko za a yi sai na gama wa’adi na.”
Maimakon sunansa, gwamna Zulum ya bu?aci a sauya zuwa “?akin kwanan ?alibai maza.”
