Sheikh Abubakar Giro Yana Raye – Izala

Wani masu neman haddasa ru?ani a tsakanin jama’a sun bada sanarwa ta karya cewa wai Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu, Wannan magana ta daga hankalin al’umma a fadin duniya, sannan mun kai karar wanda ya fara ruwaito wannan labari wajen Allah.

Sheikh Abubakar Giro Argungu yana Kasar Misrah neman magani, kuma ba’a Asibiti yake kwance ba, a gida yake zaune domin rashin lafiyar bai kai a kwantar dashi a Asibiti ba, ko yanzu munyi magana da shi ta wayar tarho, kuma har sun fara shirya-shiryen dawowa gida Naijeriya.

Dan haka ayi watsi da maganar mutuwar da ake ta yadawa.

Allah ya karawa Sheikh Giro lafiya, ya dawo mana da shi gida lafiya.

SheikhIbrahim Baba Suleiman
DG Jibwis Media & Publicity
media@jibwisnigeria.org
17-Jumada Akheer-1442
30-January-2021

Related posts

Leave a Comment