Gwamnati Na Magana Da ‘Yan Ta’adda Da Yaren Da Suke Fahimta – Ministan Labarai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce babu wani fifiko da ake nunawa tsakanin ‘yan bindiga, masu tayar da kayar baya da kuma ‘yan aware, dukkanin su ana musu azaba iri guda ne.

Lai Mohammed yana mayar da martani ne kan zargin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya tana ririta ‘yan bindiga amma kuma ba ta daga wa ‘yan IPOB da sauran ‘yan aware kafa.

Da yake zantawa da kamfanin dillacin labarai na NAN, ministan ya bayyana zargin a matsayin rashin fahimta kuma labaran bogi da aka cakuda waje daya.

Ya kuma bayyana cewa, batu ya je ga gwamnati cewa, an samu wasu da ke yada bayanan cewa, sojoji na ragargazar ‘yan IPOB amma suna sanya ga ‘yan bindiga.

A cewarsa, gwamnati ba ta banbance ‘yan ta’adda, kuma duk dan ta’adda sunansa dan ta’adda. Da yake Allah wadai da batun da ake yadawa, Mohammed ya ce: “Ina so in fadi ba tare da wani jinkiri ba cewa wannan kuskure ne. Ba gaskiya ba ne, ba daidai ba ne kuma labaran karya ne aka cakuda waje daya.

“Maganar gaskiya ita ce, gwamnatin tarayya ba ta banbance tsakanin ‘yan ta’adda da ‘yan fashi. A idon gwamnatin tarayya dukkan su masu laifi ne kuma ana bi dasu ta hanya daya. “Yana da matukar muhimmanci a daidaita batun.

Related posts

Leave a Comment