Rahotanni daga fadar Shugaban ?asa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Amurka da mutanen ?asar kan mahaukaciyar guguwar da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi shida.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ?asar, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce ya damu ?warai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana’o’i da asibitoci suka lalace.
Shugaban ya yi kira ga mutanen Najeriya su taya sauran mutanen duniya addu’a ga wa?anda suka rasa ransu da kuma samun sau?in wadanda suka jikkata.
Sama da mutum 100 ne suka rasu a guguwar wadda ta fi ?arna a jihar Kentucky ta Amurka.
