Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Mutanen ?aramar hukumar Faskari sun koka kan yadda yan fashi suka cigaba da aikata ta’addancinsu duk da ?o?arin sojoji da matakan da gwamnati ta ?auka.
An ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa matakan da ta ?auka sun fara haifar da ?a mai ido. ?ungiyoyi da kuma ?ai-?aikun mutane musamman a ?aramar hukumar Faskari sun fara ?orafin cewa yan bindiga na musu kisan mummu?e a ?auyukansu.
A wani jawabi da ta aike ofishin gwamnan jiha, ?ungiyar cigaban yankin Daudawa, ta bayyana cewa matakan da gwamnati ta ?auka ya shafi mutane fiye da yan bindigan.
Shugaban ?ungiyar, Hassan Usman, yace a halin yanzun yan bindiga suna kawo hari da sanin cewa mutane ba su da hanyar da zasu isar da bayanai ga jami’an tsaro. Yace: “Mun shiga wani yanayi na rashin tsaro mafi muni yanzu, domin mahara suna shirya kansu su kawo mana hari da kwarin guiwarsu.”
“Saboda sun san bamu da hanyar isar da bayanai, ba mu da hanyar neman ?arin jami’an tsaro.” Duk da cewa ya yaba da jami’an tsaron masu aiki a yankin, amma yace suna fuskantar ?alubale wajen neman a kawo ?auki.
Mutanen sun bayyana cewa yawaitar hare-haren da yan bindiga ke kaiwa Daudawa ya tilastawa mazauna garin da dama gudun hijira. Rahoto ya tabbatar da cewa a Daudawa ka?ai, yan bindiga sun hallaka mutum 9, sannan kuma suka yi awon gaba da wasu, bayan ?one gidaje da motoci.
Ta ya zamu bada rahoton an kawo mana hari? Wani ?an garin Daudawa, Lawal Ibrahim, ya yi kira ga gwamnati ta sassauta matakin datse sadarwa saboda mutane su samu damar bada rahoton hari.
Yace: “Lokacin da suka kawo hari Daudawa ranar Lahadi, sun fa?a mana cewa shirinsu na gaba shine zasu kai hari Unguwar Samanja, babu nisa daga nan.” Shin gwamnati tasan halin da mutane ke ciki kuwa?
Anata bangaren gwamnatin jihar Katsina ta bakin mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara ta musamman kan harkokin tsaro, yace gwamnati bata ?auki wa?annan matakan domin ta takura wa al’ummarta ba.
Ya kara da cewa gwamnati na nazari a kan tasirin matakan, kuma zata ?auki matakin da ya dace bisa duk abinda ta gano.
