Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugabannin bagaren marasa rinjaye a Majalisar Wakilai sun bi sahun takwarorinsu na Majalisar Dattawa, wajen bai wa Shugaba Muhammadu Buhari wa’adin mako shida na ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar Ndudi Elumelu, shi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa ta sirri da takwarorinsu sanatoci a ranar Alhamis.
Honorabul Elumelu ya ce muddin shugaban ya kasa daukar kwakkwaran mataki da za a ga sauyi a halin tsaron da ake ciki a kasar, za su fara daukar matakin tsigewar.
Bayan matsalar ta tsaro, shugaban marasa rinjayen ya kuma ja hankalin gwamnatin kan yanayin da kasar gaba daya take ciki, abin da ya hada da batun faduwar darajar Naira a kan kudaden waje da kuma matsalolin bangaren sufurin jirgin sama.
A ranar Laraba ‘yan Majalisar Dattawa yawanci daga bangaren marasa rinjaye suka fice daga zauren majalisar, bayan da shugaban marasa rinjayen Philip Aduda ya nemi shugaban majalisar Ahmed Lawan ya ba shi damar gabatar da bukatar tattauna batun tsaron da kuma neman tsige Shugaba Buhari.
A lokacin shugaban majalisar ya ki ba shi damar tare da cewa bukatar ba ta dace ba sam-sam, lamarin da ya harzuka marasa rinjaye suka fice daga zauren.
Bayan nan ne suka bayyana cewa sun ba shugaban kasar wa’adin mako shida ya shawo kan matsalar tsaron ko kuma ya fuskanci tsigewa.
