Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Jami’an hukumar ya?i da cin hanci EFCC sun yi dirar-mikiya a kasuwar ‘yan canji da ke unguwar Wuse Zone 4 da zimmar ya?i da masu ?oye ku?a?en ?etare, a cewar shi
Rahotanni sun ce EFCC ta ?auki matakin ne don za?ulo ‘yan kasuwar da ke saya suna ?oye ku?a?en ?asar waje musamman dalar Amurka, abin da ya sa darajar ku?in ?asar na naira ke fa?uwa a kwanan nan.
Wata majiya ta shaida mana cewa samamen ya biyo bayan shirin da suka da?e suna yi ne, inda suka dinga sa ido kan ‘yan canjin da ake zargin suna sayen dalar don ?oyewa da kuma fita da ita daga Najeriya.
EFCC ta tura jami’anta zuwa manyan filayen jirgin sama na ?asa kamar a Kano da Legas da Fatakwal da zimmar kama masu yun?urin fita da ku?in, a cewar rahoton.
A jiya Alhamis ne darajar naira ta yi mummunar fa?uwar da ba ta ta?a yi ba, inda aka dinga canzar da dala ?aya kan N705 a kasuwar bayan fage.
