Mun Ci Amanar ‘Yan Najeriya A Yi Gaggawar Kai Mu Kurkuku – Kazaure

Tsohon Ministan Aiyuka, Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya ce ya kamata Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya kama shi da sauran ?an siyasa da su ka rike madafun iko a ?aure su sabo da sun zalunci ?asar nan.

Da a ke zanta wa da shi a wani shiri a tashar rediyo ta Radio France International, Kazaure ya ce duk ?an siyasar Nijeriya ?aya su ke, inda ya ce babu wani wanda ya ke yi don talakawa.

A cewar sa, ya fa?a wa Shugaban Buhari da ya kame duk ?an siyasar da su ka wawashe ku?a?en gwamnati har da shi.

Tsohon Ministan ya ce duk ?an siyasan da su ka rike madafun iko tun daga 1999 ba su yi wa ?asar komai ba.

“Har ni da na ke wannan maganar, ya kamata a ?aure mu sabo da ba mu yi wa ?asar nan komai ba

“Na sha fa?in cewa ni Ibrahim Musa Kazaure, mun zalunci Nijeriya da talakawan ta.

“Magana ta gaskiya ita ce, dukkan mu kanwar ja ce. Abin da mu ka yi wa Nijeriya ba haka ya dace mu yi mata ba sabo da wasu daga cikin mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba.

“Ni dai gaskiya na fa?a. Dukkkan mu da mu ka yi sata, a matse mu mu dawo da ku?a?en da mu ka sata. Na fa?a wa Buhari, a kame mu a ?aure mu har sai mun dawo da ku?a?en da mu ka sata.

“Ni ba zan sake kar?ar wani mu?ami a kasar nan ba, ko da kyauta ne,” in ji Kazaure.

Related posts

Leave a Comment