Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya ce ‘yan Boko Haram ne suka tsara tare da aiwatar da hari kan jirgin kasa a Abuja zuwa Kaduna wanda ya haifar da rasa rayuka tare da garkuwa da adadi mai yawa na matafiya.
Gwamna ya bayyana haka ne a ranar Juma’a lokacin da ya ke yiwa manema labarai bayani kan sakamakon ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa.
El-Rufai ya ce harin ya yi sanadi mutuwar a?alla Fasinjoji takwas da raunatar wasu 40 da kuma garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.
Ya kuma shaida cewa an samu tattaunawa tsakanin iyalai da wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai har yanzu ‘yan bindigar ba su tambaye ku?i ba, illa daga wajen mutum guda.
Amma gwamnan ya ce yana zargin watakil daga wajen gwmanati za su neman diyya, ba daidaikun mutane ba ko iyalansu.
Gwamna El-Rufai ya ce ya shaidawa Shugaba Muhammadu Buhari cewa salon harin ‘yan bindigar na wannan lokaci ya bambanta da wanda aka saba gani a baya saboda ‘yan Boko Haram ne suka taimakawa ?arayin dajin.
Sannan a halin da ake ciki yanzu jami’an tsaro na duba inda suke ?uya domin yi musu kawanya don daukar matakan da suka dace.
