Za Mu Magance Matsalar Sabbin Kudi Nan Da Mako Guda – Buhari


Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bu?aci ?an ?asar da su ba shi kwanaki bakwai kacal domin shawo kan matsalolin ku?i da suke kawai tasgaro a ?asar.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani taro da ya yi da ?ungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC wa?anda suka je fadar shugaban ?asar domin neman mafita kan ?arancin ku?in da ake fama da shi wa?anda suka ce hakan na barazana kan ayyukan alkhairi da gwamnatin ta yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ?asar Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya ce sauya fasalin ku?in da aka yi zai ha?aka tattalin arzikin ?asar da kuma samar da tagomashi na tsawon lokaci ga ?asar.

Haka kuma shugaban ya nuna damuwa kan lamuran wasu bankuna a ?asar inda ya ce kansu ka?ai suka sani kuma a cewarsa ko shekara guda aka ?ara, matsalolin da suke tattare da san kai da zari ba za su gushe ba.

Hakan bai rasa nasaba da kalaman da gwamna El Rufai ya yi a wata hira da BBC inda ya ce akwai wani gwamna daga cikin gwamnonin ?asar da ya samu sabbin ku?i har naira miliyan 500.

Related posts

Leave a Comment