Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 17 A Daren Azumi

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun kashe a?alla mutum 17 a wani hari da suka kai ?auyuka hu?u na karamar hukumar Anka jihar.

Mazauna yankin sun ce mutanen ?auke da makamai sun farmaki ?auyen Kadaddaba da tsakar rana, suka bu?e wa mutane wuta. Sun bayyana cewa ba bu wani abu na tsokanar fa?a da yan kauyen suka yi da ya jawo yan ta’addan suka kai harin.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Hussaini Muhammad ya ce: “Sun shigo a kan Mashina suka bu?e wa mutane wuta. Muna fitowa daga Sallan Azahar muka hangi tawagarsu na ?arasowa, nan take muka ankarar da na kusa muka tsere jeji.”

“Sun bi mutanen dake kokarin guduwa, duk wanda suka cimma su harbe shi, sun ?ashe mutum 10 a ?auyen mu cikinsu har da sirikina. A Rafin Doka sun kashe mutum ?aya, biyu a Babban Baye, a Wano kuma mutum hu?u.”

“Ba wani nisa mutane suka yi ba, yanzu da nike magana da ku ina Anka na je gudun Hijira.’

Mutumin ya ?ara da cewa tun da farko yan bindigan sun shiga kasuwar Rafin Gero suka yi awon gaba da dabbobi da yawa wa?anda mutane suka kawo domin siyarwa.

“Sun ?wace Shanu da sauran dabbobi suka tasa zuwa Jeji. Haka nan sun fasa shaguna sun ?ibi kayayyaki, akwai labarin da yace sun kashe mutane amma ban san adadin su ba.”

Har yanzun da muke ha?a wannan rahoton ba’a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, ba.

Related posts

Leave a Comment