Rahotanni daga fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar dake Jihar Sokoto na bayyana cewar kwamitin duban wata ya sanar da cewa an ga watan azumin Ramadan na shekarar 2022 a wasu sassan ?asar da yammacin ranar juma’a.
Hakan ya tabbatar da cewa yau Asabar 2 ga watan Afrilun 2022 aka tashi da azumin a matsayin 1 ga watan Ramadan na shekarar 1443 bayan Hijira.
Sanarwar ganin watan ya zo ne bayan da ?asar Saudiyya ta sanar da nata ganin watan tun da yammacin ranar ta Juma’a 1 ga watan Afrilun, wato sa’o’i kadan kafin ganin na Najeriya.
Kwamitin ganin watan wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Tuwita ya ce an gan shi ne a garuruwan Bauchi da Gombe da Azare da Misau da Numan da Legas da Kaduna da Abuja da Bajoga da Nafada da kuma birnin Maiduguri da wasu da dama.
