Gangamin Jam’iyyar APC: PDP Ta Gargadi Hukumar Zabe

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta gargadi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kada ta halarci taron gangamin jam’iyya mai mulki APC ko sanya ido kan lamarin a yayin taron da za ta gudanar.

Babbar Jam’iyyar adawan ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da kakakinta Debo Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris aka rarraba wa manema labarai a Abuja.

PDP ta bayyana taron na ranar Asabar 26 ga watan Maris a matsayin taron hauragiya da jam’iyyar mai mulki ta shirya, inda suka yi gargadin cewa hukumar zabe za ta fita daga dokokinta na kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar halarta ko kuma sanya ido a taron da APC ta shirya.

PDP ta yi zargin cewa APC ta daina fita bisa ka’ida tun bayan da ta rusa tsarukanta na kasa, jihohi da kananan hukumomi a ranar 8 ga Disamba, 2020 kuma ba ta gaza wajen bin dokokin INEC.

A bangare guda, PDP ta shawarci ‘yan Najeriya da ke da niyyar halartar taron da su nemi jagoranci, tare da lura da cewa suna tafiya ne da ba za su san inda za a je dasu ba.

Related posts

Leave a Comment