Rahotannin da muke samu na tabbatar da cewar dakarun sojin Nijeriya, ha?in guiwa da hazi?an jami’an kwantar da tarzoma (Mopol) da jaruman ?an banga, sun yi wa barayi masu garkuwa da mutane da suka addabi al’ummar ?aramar hukumar Mariga da ke waye ruwan wuta.
Da yammacin yau ne jami’an tsaron suka yi wa ?an ta’addan ruwan wuta ta sama da ?asa a dajin Ma’undu dake gundumar Beri. Inda jirgin ya?i ke sakarwa barayin bama-bamai, yayin da mopol da ?an banga ke ragargazar barayin ta ?asa. Kawo izuwa yanzu babu al?alumman ?an ta’addan da aka kashe, saidai muna da ya?inin hukumomin dake da alhakin hakan zasu yi a duk lokacin da suka tattara al?aluman su a hukumance.
Ha?i?a jaruman jami’an tsaron mu sun cancanci yabo, da jajirtattun wakilan Jihar Neja irin su Sen. Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa wanda yake tsaye ?yam domin ganin an shawo kan wannan matsala. Kuma wannan mataki da gwamnati ta ?auka zai fara sanya kwanciyar hankali a zukatan talakawa, na cewar gwamnati da gaske takeyi.
Allah ya ?ara bamu zaman lafiya.
