Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyoyin mata daban-daban sun ba wa Majalisar Tarayya wa’adin kwanaki bakwai cewa su amince da ?udirin Gyaran Dokar Jinsi biyar, wadda makwannin baya su ka yi watsi da su.
Matan sun yi wannan kiran ne a taron Manema Labarai da su ka yi a Abuja, bayan sun dakatar da zanga-zangar da su ke yi kullum bakin ?ofar Majalisa a Abuja.
A watan Maris ne Majalisa ta ?i amincewa da yi wa Dokar Jinsi gyare-gyare guda biyar da aka gabatar a majalisa, wa?anda za su gyara matsalolin da ke damun mata a dokokin Najeriya.
Tun daga washegarin yi fatali da ?udirin ?ungiyoyin mata daban-daban su ka ri?a yin zanga-zangar zaman dirshan a ?ofar shiga Majalisa, har tsawon kwanaki 10 na zaman majalisa.
Matan su na neman ko ana ha-maza-ha-mata sai an amince da ?udirin, an yi wa dokakin biyar kwaskwarima.
