Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar kula da ayyukan yan sandan Najeriya, PSC, Musiliu Smith ya yi murabus daga aikinsa, an ruwaito cewa kwamitin hukumar ne ta bukaci Smith ya yi murabus kuma ya amince.
Wani majiya mai tushe ya shaidawa majiyarmu ta Jaridar Daily Trust cewa Smith, tsohon sufeta janar na yan sanda, zai mika mukamin ne ga tsohon alkali Clara Ogunbiyi da ke wakiltar bangaren shari’a a hukumar.
Hukumar ta rika kai ruwa rana da ofishin sufeta janar na yan sanda kan wanene ke da hurumin daukan sabbin jami’an yan sanda. Hukumar ta PSC ta tallata daukan sabbin jami’an yan sanda kuma ta bukaci masu sha’awan aikin su ziyarci shafinta na intanet su cike fom. Amma, rundunar yan sandan ta bukaci al’ummar kasa su yi watsi da sanarwar, ta dage cewa rundunar ce ke da hurumin daukan sabbin jami’an yan sanda.
