Filato: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Takarar PRP A Mazabar Jos Ta Arewa

Rahoton dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Kotu dake saurarar karararakin za?e dake zamanta a kotun High Court 4, Jos a ranar Juma’a ta fitittiki Musa Avia Aggah, dan majalisar wakilan tarayya na jam’iyyar PDP.

Musa Avia Aggah ya kasance mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilai. Kotun ta bayyana cewa ba Agah bane halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP a zaben ba.

A hukuncin da Alkalan kotu Justice Hope O. Ozoh. Khadi Usman Umar, da Justice Zainab M. Bashir, suka yanke, lauyoyin Gwani Alkali sun tabbatar da gaskiya. Saboda hakan, kotun ta alanta Goni Muhammad Adam Alkali na jam’iyyar PRP a matsayin wanda yayi nasara.

Related posts

Leave a Comment