Adamawa: Dan Luwadi Ya Yi Yunkurin Kashe Kanshi Bayan Shiga Hannu

Rundunan ‘yan Sandan jkhar Adamawa ta kama wani mutum dan shekaru 45 da haihuwa bisa zarginsa da yin luwadi da wani yaro ?ana shekaru goma da haihuwa a ?aramar hukumar Mayo Belwa dake jihar.

A wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hannun Kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar SP Suleiman Yahaya Nguroje na cewa an samu nasarar kama wanda ake zargin ne biyo bayan kara da Mahaifin yaron wato Akure Usman tare da wasu mutane suka kai ofiahin ‘yan sanda dake Mayo Belwa inda Jami’an ‘yan sandan basu yi da wasa ba wajen kama wanda ake zargin.

Shidai wanda ake zargin mai suna Kawu Sale wanda yake zaune a anguwar Tsohon Tike a cikin garin na Mayo Belwa ya yaudari yaron ne zuwa dakinsa da sunan zai bashi kayan sawa.

A yayin da aka zo kama wanda ake zargin yayi yunkurin hallaka kansa da wuka inda ya yanka wuyansa da kuma jiwa cikinsa ciwo da wuka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Adamawa Sikiru Kayode Akande tuni ya bada umurnin gudanar da bincike kuma yace da zarar sun kammala bincike za a gurfana dashi gaban kotu domin ya fuskaci Shari a.

Related posts

Leave a Comment