Ilimi: Yajin Aikin ASUU Ya Haura Kwanaki 200

A ranar jiya Juma’a ne aka cika kwanaki 200 cif, da fara yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta tsunduma.

A tsawon wannan lokacin dai an yi ta zama teburin sulhu tsakanin gwamnati da ASUU amma ana tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Wasu daga cikin daliban da yajin aikin ya shafa, sun shaidawa BBC cewa ba su zaci lamarin zai kai tsahon wannan lokacin ba.

Daya daga cikinsu mai suna Ummi Musa, daliba a jami’ar Bayero da ke Kano ta ce: ”Muna tsaka da zana jarabawa aka tafi yajin aikin, daga farko gaskiya mun dan ji dadi, ganin cewa za mu samu karin makonni biyu na sake karatu.

Amma da aka wuce wannan lokacin sai muka gane shayi ruwa ne, lamarin nan ya janyo mana cikas a karatu, musamman ni da ke shekara ta 4, a fannin shari’a.

Dan Allah gwamnati da ASUU su taimaka mana, saboda ni dai a yajin aiki aka haife ni, na girma acikinsa yau gashi har yazo kai na, idan tun daga wancan lokacin da malamai ke tafiya yajin aiki ba su yi galaba ba, kenan matakin ci gaba da yajin aiki ba zai sauya komai ba.”

Ita wata daliba mai suna Shema’u Muhammad ta bayyana cewar saboda zaman gida da ya tura, har iyaye sun fara yi musu batun aure tun da karatun bai samu ba.

A watan Fabrairun 2022 ne dai malaman jami’o’in Najeriyar suka tafi yajin aiki, kan rashin biya musu bukatu da gwamnatin Najeriya ta yi da suka hada da alawus-alawus da karin albashi da sauransu.

A ?angaren Malaman jami’o’i kuwa da yawa sun shiga cikin halin kunci da tasku sakamakon rashin biyan su albashi na tsawon watanni shida, inda kungiyar ta ASUU ta bayyana cewar wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar sun rigamu gidan gaskiya dalilin wahalar rayuwa.

Related posts

Leave a Comment