An Haramta Wasan Tashe A Kano

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta haramta “Tashe”, wani wasan barkwanci da ake yi duk shekara bayan kwanaki goma na farkon watan Ramadana.

Kakakin rundunar, SP Abdullaji Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a wata takarda da rundunar ta fitar ranar Litinin kuma aka rarraba ga manema labarai a Kano.

Kamar yadda takardar ta bayyana, dalilin da yasa aka haramta al’adar mai cike da tarihi shine yadda hatsabibai ke amfani da damar wajen cutar da al’umma da sauran abubuwa marasa dadi.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Kano na burin sanar wa da daukacin al’umma cewa ta dakatar da wasan barkwancin nan da aka dauki tsawon zamunna ana yi (Tashe), wanda ke zuwa duk bayan kwana goma na watan Ramadanan kowacce shekara.

“Dalilin hakan kuwa shine yadda hatsabibai ke badda kama da sunan “Tashe” don aikata munanan ayyuka irinsu sara-suka, kwacen waya, da ta’ammuli da miyagun kwayoyi.”

Ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya yi kira ga mutanen jihar Kano, musamman iyaye da marika da su ja kunnen ‘ya’yansu kada su yarda a kamasu da laifin karya kowacce irin doka da ka’ida.

Related posts

Leave a Comment