Farashin Fom Din Takarar APC Ya Razana ‘Yan Najeriya

?an Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan tsadar fom na takara a jam’iyyar APC inda ta ke sayar da fom ?in takarar shugaban ?asa a naira miliyan 100.

A ranar Laraba ne majalisar zartarwar jam`iyyar ta tabbatar da jadawalin zabukan fitar da gwani na masu neman mukamai daban daban da kuma farashin fom na takara.

Majalisar zartarwar jamiyyar ta yi zaman ne ?ar?ashin jagorancin shugaba Buhari da shugabannin jamiyyar na kasa da jihohi da gwamnoni da sauran jiga-jiganta daga sassan Najeriya inda aka amince da farashin fom na neman takara da ranakun da za a gudanar da zabukan fidda gwani.

A sanarwar da APC ta fitar ta ce masu son yin takarar shugaban ?asa za su biya ku?in na-gani-ina-so naira miliyan 30, sai kuma ku?in fom naira miliyan 70.

Masu son yin takarar gwamna za su lale naira miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya miliyan 20.

Masu fatan zama ‘yan majalisar wakilai za su biya naira miliyan 10. ?an majalisar jiha miliyan biyu.

Related posts

Leave a Comment