Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban ?asa a Najeriya, Adamu Garba, ya ka?u da jin farashin fom ?in takararar da jam’iyyarsu ta saka na naira miliyan 100.
A yau Laraba ne APC ta ce duk mai son ya tsaya takarar shugaban ?asa sai ya biya ku?in na-gani-ina-so naira miliyan 30 da kuma ku?in fom naira miliyan 70.
Adamu Garba ya bayyana ka?uwarsa ne a shafinsa na Twitter jim ka?an bayan sanar da farashin.
“Miliyan 100 ku?in fom. Lallai!,” kamar yadda ya wallafa.
Matashin da ke yawan amfani da shafukan zumunta ya kuma nemi ‘yan uwansa matasa su fito su “ya?i jakunkunan ku?i”.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da sayen ofisoshin gwamnati a Najeriya ba, muna bu?atar ?wararrun shugabanni a (za?en) 2023,” in ji shi.
