“Babu wani dan fim da ya Isa na raga masa ,don haka duk wanda ya taka ni sai na taka shi, kuma duk wanda ya yi mun rashin mutunci, to sai na mayar masa, dona haka bazan ragawa kowa ba.”
Wannan furicin ya fito ne daga bakin fitaccen jarumin Barkwanci Aminu Baba Ari, a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, a kan yadda zaman masana’antar ya ke a halin yanzu.
Ya ci gaba da cewa “Ita masana’antar fim akwai shika shikai na zama a cikin ta, har guda Goma zan iya fada maka guda biyar, amma sauran biyar din zan boye su ba zan fada maka ba.” Inji shi.
Ya Kara da cewa, “Na farko akwai bakin ciki, akwai Hassada, akwai mugunta, akwai ganin kyashi. Wadanda su ne guda biyar, sauran kuma sai wata rana zan fada maka” a cewa Baba Ari.
“Don haka ka sani zaman cikin harkar fim duk akwai wadanda abubuwan, Idan har ba ka iya ba to zaman sai ya ga gare ka, don haka na ce da kai ba na saurara wa kowa, idan mutum ya zo mun da rashin mutunci, to fa sai na yi masa. Amma Idan mutum ya zo mun da hanyar zaman Lafiya, to nan ma ya samu zaman Lafiya, donmin komai mun iya da rashin mutunci da kuma mutuncin. Ba mu gaji rashin arziki ba, Amma zaman Duniya ya koya mana shi. “kamar yadda ya bayyana.
Mun Kara tambayar sa ko shi ne ya sa ke jin yana yin habaici, da gugar zana a cikin wasan na sa na Barkwanci?
Sai ya ce “wannan ba haka ba ne, duk wanda ka ji na kama sunan sa ba don ya bata mun ba ne wasan ne kawai ya zo da haka, amma wani lokacin idan ka ji ina ta yabon mutum, to ya yi mun abin arziki ne, domin ni ba na manta abin arziki, saboda gidan mu gidan arziki ne, don haka duk wanda ya yi mun abun arziki ba na mantawa da shi. ” Inji Baba Ari.
A karshe ya yi kira ga abokan sana’ar shi na fim cewa,” lokaci ya yi da za su hada kan mu, don mu fuskanci Matsalolin da masana’antar take ciki a yanzu, domin a samar da mafita a cikin harkar”
