Ba Zan Bari A Sake Karya Doka A Najeriya Ba – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji mutanen da ke hankoron ganin sun karya doka a kasar.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ta ambato Shugaba Buhari yana mai tabbatar wa ‘yan kasar cewa ba zai kyale wani ya karya dokokin kasar ba.

”Muna da kasa, muna da albarkatun kasa da kuma mutane. Sai dai ban san dalilin da ya sa wasu ke da niyyar ba da kansu ba wajen lalata ?asarsu ba,” a cewar Buhari yayin bu?e baki da ya yi da gwamnoni da ministoci a Abuja ranar Talata.

Shugaban ya sake jaddada cewa ?addamar da amfani da fasahar na’urar tantance masu ka?a ?uri’a “ba za ta bari wani ya yi i?irarin samun miliyoyin ?uri’u” yayin babban za?e na 2023 mai zuwa.

Related posts

Leave a Comment