Biyo bayan kisan matafiya sama da 20 da da wasu bata gari suka yi a Jos Fitaccen dan kwallon kafa, Ahmed Musa, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da tayi saurin tashi tsaye ta kula da rayuka da dukiyoyin al’umma domin aikinsu ne yin hakan.
Ahmed Musa ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da tayi gaggawar kawo karshen yadda ‘yan bindiga da sauran bata gari suke kashe ‘yan Najeriyan da basu ji ba basu gani ba.
Dan kwallon mai shekaru 28 ya yi tsokacin ne a shafinsa na Instagram a kwanakin karshen mako yana bayyana takaicinsa akan kisan da aka yi wa mutane 22 wadanda suke hanyarsu daga Bauchi daga wani taron addini.
Kamar yadda Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na Instagram: Kashe-kashe da aka yi wa matafiyan nan da suka taho daga Bauchi bayan sun kammala zikirin sabuwar shekarar musulunci suna hanyar komawa gidajensu yayin da aka kai musu farmaki a titin Rukuba na Jos ta arewa abin takaici ne.
Ina kira ga gwamnati da duk wasu hukumomi da ya kamata su samar da tsaro a kasar nan da su yi gaggawar kawo dauki don hana irin wannan lamari faruwa. Muna musu fatan rahama kuma Ubangiji ya samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu da Najeriya baki daya.
