Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Ziyarar Aiki A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana bayan saukar Sakataren Majalisar Guterres ya ziyarci birnin Maiduguri na jihar Borno da har yanzu ke fama da matsalar hare-haren mayakan Boko Haram da na ISWAP da suka balle daga kungiyar.

Yayin ziyarar tasa a Borno, sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya gana da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum a birnin Maiduguri, daga bisani kuma ya gana da wasu daga cikin iyalan da rikicin Boko Haram ya shafa tsawon fiye da shekaru 10.

Daga jihar ta Borno, Antonio Guterres ya tashi zuwa birnin Abuja,  inda zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

A birnin na Abuja Guterres zai ya jagoranci wani bikin alhini da kuma karrama wadanda suka rasa. rayukansu yayin harin bam din da aka kai kan ginin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2011. Daga nan kuma zai gana da wakilan kungiyoyin mata da matasa, da kuma shugabannin addinai da ‘yan jarida.

Wannan dai shi ne karo na farko da Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ke ziyartar Najeriya tun bayan hawansa kan mukamin.

Related posts

Leave a Comment