NNPCL Zai Gurfana Kotu Dalilin Bacewar Dala Biliyan 2.04 Da Naira Biliyan 1644

images (18)

Kungiyar SERAP ta shigar da ?ara kan kamfanin NNPCL saboda gaza bada bayanan ku?in shiga na man fetur $2.04bn da N164bn da suka ?ace. A cewar SERAP ta shigar da ?arar ne bisa zargin da babban mai binciken ku?i na tarayya ya fitar a rahoton binciken shekarar 2020.

rahoton ya yi zargin cewa kamfanin NNPCL ya gaza sanya ku?a?en cikin asusun tarayya, inda ya ce ta yiwu an karkatar da ku?a?en ne.

Rahotanni sun bayyana cewa an shigar da ?arar ne mai lamba FHC/ABJ/CS/549/2024 a ranar Juma’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A cikin ?arar SERAP ta bu?aci kotun da ta umurci tare da tilastawa NNPCL ya yi bayanin inda $2.04bn da N164bn na ku?a?en shiga na man fetur, kamar yadda yake a cikin rahoton babban mai binciken ku?i, rahoton Channels tv ya tabbatar. SERAP ta kuma bu?aci NNPCL da ya mi?a masu hannu a cikin zargin ga hukumomin ICPC da EFCC domin bincike da gurfanar da su. Ta kuma bu?aci NNPCL ya tabbatar da kwato ku?a?en da suka ?ace domin mayar da su zuwa asusun tarayya.

Related posts

Leave a Comment