Daruruwan Matasa Za Su Samu Aiki A Matatar Mai Na – Dangote

Shugaban kamfanin ?angote Group, Aliko ?angote, ya ce sabuwar matatan man Fetur ?in da ya gina zata samar da, “?umbin ayyukan yi,” ga matasan Najeriya. ?angote ya bayyana haka ne ranar Litinin a Legas, a wurin bikin kaddamar da matatar man mai suna, “Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals.”

Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci bu?e matatar man fetur ?in, wacce ake sa ran zata samar da isasshen mai ga Najeriya.

Haka zalika ana tsammanin Matatar ?angote zata ri?a aikin samar da Man Fetur, Man Dizel, Man jiragen sama, kalanzir da sauran makamantansu.

“Haka nan matatar zata samar da isasshen muhimman kayan aiki ga Masana’antun ha?a magunguna, abinci, kayan sha, gine-gine da sauran ma’ana’antu a ?asar nan.”

Fitaccen ?an kasuwan ya bayyana godiyarsa bisa ?umbin goyon bayan da ya samu a karan kansa da kuma kamfaninsa Dangote Group yayin gina wannan matata. Ya yaba wa shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, da sauran ‘yan Najeriya bisa goyon baya mara misaltuwa da suka nuna masa tun daga kafa tubalin ginin har zuwa yau da aka kammala.

Related posts

Leave a Comment