An bayyana cewar jama’ar Jihar Kaduna a halin yanzu suna cikin wani mawuyacin hali ne na rai kwakwai mutu kwakwai sakamon ukubar da gwamnan jihar El Rufa’i ke dandana musu a tsawon lokaci, babu wata mafita garesu a yanzu sai addu’a da fatan cikawa da Imani.
Sakataren Jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Ibrahim Wusono ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci dangane da halin rayuwa ta lahaula da jama’ar Jihar Kaduna suka tsinci kansu a karkashin mulkin El Rufa’i.
Wusono ya cigaba da cewar babu abin da jama’a suka girba a canjin da suka yi wa kansu a shekarar 2015 zuwa yanzu sai azaba, ukuba talauci da tsananin jin jiki mara misaltuwa.
“El Rufa’i ya kashe komai a jihar ya jefa jama’a cikin azabar da basu ta?a gani ba a tarihin Jihar Kaduna, bayan korar Ma’aikata babu ji babu gani da yake yi, ga rurrusa kasuwanni da gidajen al’umma, abin da sai dai ace Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un”.
Wusono ya kalubalanci Malamai wa?anda a baya lokacin Mulkin PDP suka ri?a hawa munbarorin masallatai suna wa’azi akan cewar zabar APC jahadi ne, da yin alkunuti ga PDP, da cewar a halin yanzu me yasa aka ji sun yi shiru ba sa wa’azin la’antar ba?in mulki dake faruwa a ?asar?
Daga karshe Jigon jam’iyyar PDP din ya shawarci Jama’ar Jihar da suyi amfani da kuri’unsu a za?en dake wajen kawar da mulkin zalunci, sannan su bi tsarin nan na “A kasa a raka a jira” domin tabbatar da samun abin da suka zaba.
