Rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane biyu wadanda suna ciki wadanda suka gudu daga gidan gyara hali dake Kuje a Abuja.
Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda kuma aka rabawa manema labarai a Yola.
Mutanen dai sune Atiku Ibrahim mai shakaru talatin da bakwai da haihuwa sai Adamu Ibrahim mai shekaru Arba’in da haihuwa wadanda sun gudu daga gidan gyara halin ne biyo bayan hari da aka kai a gidan yarin na Kuje a Ranar 5-6-22. Wanda yayi sanadiyar mazauna gidan yarin akalla dari biyar suka gudu.
Kuma ana tsare da sune bisa zarginsu da satan shanu dama sauran laifuka wanda kuma suna zaune a gidan yarin ne tun daga shekara ta 2021.biyo bayan zarginsu da safaran makamai kuma sun tabbatarwa rundunan jihar Adamawa cewa suna cikin wadanda suka gudu daga gidan yarin kuje.
Kuma sun bayyana cewa suna ma zaman jiran Shari’a ne a gidan yarin bisa zarginsu da safaran makamai.
Kawo yanzu dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurni da a gaggauta mika su ga hukumar dake kula da gidajen gyara hali dake jihar ta Adamawa domin daukan matakin da ya dace.
