Ina Da Tabbacin Tinubu Zai Dora Daga Inda Muka Tsaya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Legas na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin ya ce ya yi farin ciki da barin tattalin arzi?in Najeriya a hannun ?wararru. Shugaban mai barin gado ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a wajen ?addamar da matatar man Dangote a Legas.

“Wannan babbar masana’anta da muke ?addamarwa a yau misali ce ?arara na abin da za a iya samu idan aka ?arfafawa ‘yan kasuwa gwiwa da tallafa musu da kuma idan aka samar da yanayin da mutane za su iya saka hannun jari don ci-gaban kasuwanci.”

Buhari ya ?ara da cewa ya na kyautata zaton cewa za?a??en shugaban ?asar mai jiran gado zai cigaba da yin abubuwan da za su taimaki tattalin arzi?in ?asa A fa?arsa: “Ina da ya?inin cewa mutumin da zai gaje ni, mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai ci gaba da inganta tattalin arzi?inmu da kasuwancinmu, tare da bin tsarinmu na ?arfafa ala?a tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa don ?ara ha??aka tattalin arzi?inmu da bunkasa shi cikin gaggawa.”

“Ina kira da ?arfafa gwiwar sauran manyan ‘yan kasuwanmu da su yi koyi da wannan fitaccen ?an kasuwan, su ha?a hannu da gwamnati wajen ?ara ha??aka ci gabanmu domin tabbatar da ?arfin tattalin arzikin da ake kallon ?asarmu da shi a duniya.”

“Lokacin da na zagaya Afirka kuma na ha?u da ‘yan’uwana shugabannin ?asashe (kuma naji da?i wasunsu suna nan wurin), sau da yawa nakan ji a raina cewa ?asarmu na da albarkatu da jarin ?an adam domin jagorantar ha?aka tattalin arzikin Afrika, cigaba da kuma cimma burin 2063, na ‘Afrikar da dukanninmu ke so.’”

Related posts

Leave a Comment