Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewa kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin binciken kan rikice-rikicen siyasa ya fara zamansa na jihar.
Kwamitin karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf, zai yi bincike ne a kan rikice-riciken siyasa da mutanen da suka ?ata da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da kuma 2023.
A cikin jawabin da ta gabatar a lokacin ?addamar da zaman farko na kwamitin, Zuwaira Yusuf ta ce kwamitin zai yi ?o?arin za?ulo wa?anda suka ?auki nauyi da kuma wa?anda suka aikata laifukan da suka shafi rikicin siyasa da kuma sauran ayyukan assha.
Haka nan kwamitin zai bayar da shawara kan yadda za a tallafa wa mutanen da rikice-rikicen suka rutsa da su.
