?an bindiga sun kashe ?aya daga cikin faston cocin katolika a Kaduna da aka sace bayan sun kar?i ku?in fansarsa.
A wata sanarwa da cocin katolikan ta fitar, ta ce an gano gawar rabaran John Mark Cheitnum a ranar Talata.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Kaduna ya shaida wa BBC cewa masu garkuwa da mutanen sun kar?i ku?in fansa.
Ya ce bayan da suka kar?i ku?in fansar sai suka yi musu kwatancen wurin da gawar faston take.
Sai dai ?an bindigar sun saki ?ayan faston da suka yi garkuwa da shi wato Rabaran Donatus Cleopas.
Babu tabbaci kan dalilin da ya sa aka harbe ?ayan faston. An yi garkuwa da fastocin biyu ne a ?auyen Yadin Garu a ranar Juma’ar da ta gabata.
Tun daga watan Mayun bana, an yi garkuwa da gwamman malaman Addinin Kirista wa?anda akasarinsu mabiya ?ari?ar katolika ne.
