Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yammacin ranar Laraba ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi hatsarin mota a Abuja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mukarrabansa biyu nan take.
?aya daga cikin masu taimaka masa, wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin, ya ce Jonathan na cikin koshin lafiya a halin yanzu.
Hadarin ya afku ne a lokacin da tsohon shugaban kasan ke kan hanyar sa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe zuwa gidansa da ke Abuja.
A cewar majiyoyi daga makusanta Jonathan, har yanzu tsohon shugaban kasar yana Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, har zuwa safiyar Laraba. An ce ya tafi Abuja ne domin wani aiki a hukumance.
