An bayyana dumamar Yanayi da Kuma dabi’ar zubar da shara barkatai a matsayin wasu hanyoyi dake barazana ma muhalli tare da haifar da mummunar ambaliyan ruwa a mafi yawanci garuruwa musamman a Najeriya da sauran kasashen duniya
Shugaban Hukumar kula da tsaftace muhalli na Jihar Dokta Ibrahim Kabir ya bayyana haka ma manema labarai a lokacin da yake zagayen duba share muhalli da hana zirga-zirgan ababen hawa na karshen ko wani wata dake gudana a fadar Jihar.
Shugaban yace “a hukumance muna yin iya bakin kokarinmu domin mukwashe datti a magudanan ruwa da gefen hanyoyi, da kuma sako-sako da lungu-lungu musamman inda Jama’a suke don kaucewa yaduwar cuta da barazanar ambaliyar ruwa a sanadiya ruwan sama Mai karfin gaske”.
Kana ya Kara da cewa, “har ila yau muna kokarin sake tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan kwashe ma gudanan ruwa da ci gaba da fadakarwa tare da jan’kunne gami da hatsarin dake tattare da zama cikin datti konrashi share datti a cikin al’umma”
Dokta Kabir, yace yanzu haka muna cikin kwamitin da Gwamna ya kafa don kaucewa ambaliyar ruwan nan gaba, yace kamar yadda ambaliyar tafi ta’azzara a Karamar hukumar Kirfi yanzu haka har aikin kwamitin yayi nisa a cewar sa abu ne wanda ya shafi al’umma Kai tsaye,
Kabir yace hakan yasa dole ne su tashi haikan domin ceto mutane daga ambaliyar ruwan tare da hadin gwiwar ma’aikatar Kai tallafin gaggawa da tausayawa ta Jihar Bauchi.
Ya Kara da cewa aiki ne wanda zai lakume kudi masu yawan gaske, Kuma gwamnatin jihar Yusuf tace zata yi, yace shiyasa suka shigo da babban bankin duniya a cikin wani babban aiki da zasu gudanar a cikin Jihar.
#
