Ba Kudi Muke Bukata Ba – ‘Yan Fashin Jirgin Abuja

A karon farko, ‘yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ?asan fasinja da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun yi jawabi, inda suka yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matu?ar gwamnati ba ta biya musu bu?atunsu ba.

A jiya ne, wani bidiyo da ya bayyana, ya nuna wasu daga cikin maharan ?auke da bindigogi suna i?irarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ?asan a ranar Litinin din makon jiya.

Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna hu?u cikin ‘yan bindigar sanye da kakin sojoji, rufe da fuskoki a tsaye suna i?irarin ci gaba da ri?e fasinjojin jirgin ?asa da suka sace a ?arshen watan jiya.

Ba a dai ga fasinjojin a cikin ta?aitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna ri?e da su.

Sun kuma ce ba za su sake su ba har sai gwamnati ta biya musu bu?atunsu, amma ba su bayyana bu?atun nasu ba.

Wani cikin masu jawabin ya ce ba bu?atar ku?i ce ta sanya su sace fasinjojin ba, suna masu yin i?irarin cewa gwamnati ta san bu?atun.

Bidiyon ya nuna maharan ne tare da Alwan Ali Hassan, daya daga cikin fasinjojin da aka sace a jikin wata motar igwa da wuta ta cinye ?urmus, a wani wuri mai bishiyoyi.

An sako shi ne da yammacin jiya Laraba, kwana tara bayan wani hari kan jirgin ?asan fasinja da ke tafiya zuwa Kaduna.

Maharan sun ce sun saki Alwan Hassan ne saboda tausayin tsufa da kuma alfarmar azumin watan Ramadan.

Sai dai wasu kafofin labarai sun ce sai da aka biya miliyoyin naira kafin sakin nasa.

A cikin bidiyon, an ji Alwan Hassan yana cewa an sake shi ne saboda tsufa amma ya bar wasu mutanen da dama a can.

Ya kuma ce mutanen da ya baro suna cikin bu?atar ?auki.

Hukumar kula da sufurin jiragen ?asa ta Nijeriya ta ce fasinja 162 ne suka ?ata bayan harin na ranar Litinin.

Babu tabbaci ko duka wannan adadi ne ke can a hannun maharan.

Bidiyon dai bai yi ?arin haske a kan ?ungiyar da ta kai harin ba, wadda kwanan baya, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’i ya ce Boko Haram ce.

An dai ji mai magana na farko cikin ‘yan bindigar da suka yi magana a bidiyon na bu?e jawabi da wasu kalamai na Larabci, kafin ya ?ar?are da hamdala.

Related posts

Leave a Comment