Shugaba Muhammadu Buhari zai je Habasha don halartar taron rantsar da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed a wa’adinsa na biyu ranar Litinin a Addis Ababa.
Shugaban zai bar Abuja ranar Lahadi zuwa babban birnin Habasha kuma ana sa rai zai gabatar da jawabin fatan alheri a taron rantsuwar.
Daga nan kuma zai halarci liyafar cin abinci tare da sauran shugabannin ?asashe.
Ministan harkokin ?asashen waje Geoffery Onyeama da Shugaban Hukumar Le?en Asiri ta NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar ne za su yi wa Shugaba Buhari rakiya.
Zai dawo Abuja ranar Talata.
