Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya ce alanta mulkin shugaban kasa ga yanki zai iya sa kasar nan ta kare da ‘yan takara biyu marasa amfani a 2023.
A yayin jawabi a Arise TV a ranar Juma’a, Sanusi ya ce sau da yawa ya na kushe duk wata tattaunawa da za a yi kan yankin da ya dace ya samar da shugaban kasa, domin kaucewa shiga ru?ani.
Manyan jam’iyyu biyu na kasar nan na APC da PDP suna ta cece-kuce kan yankin da zai samar da shugaban kasa. Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce Najeriya ta na bukatar shugaban kasa wanda zai iya amfanar ta ba tare da duban yankinsa ba.
“A koyaushe ina kushe wannan ra’ayin na cewa sai an mayar da hankali an ga inda shugaban kasa zai fito. Akwai gwamnonin kudu da ke cewa suna son shugabancin kasa da kuma gwamnonin arewa da ke cewa suna son arewa ta yi shugabancin kasa.
Kun lura cewa babu wanda ya bayyana abinda ya ke so?” Yace. “Duk wannan abun ana yin shi ne don killace shugabancin kasan zuwa wani yankin kasar kuma babban dodon zai bayyana. Hakan yasa a karshen al’amarin sai a kare a Najeriya ta fitar da ‘yan takara biyu marasa amfani.”
“Babban gazawar kasar nan bamu dubawa. Mun fi wayau idan aka yi batun kudi amma ba mu saka tunanin mu inda ya dace. “Ku bani shugaban kasa daga kowanne yankin kasar nan wanda zai iya yin abinda ake so kuma za mu zabe shi. Ba shugabancin kasan zai dauka ya mayar kauyensu ba.”
