Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Karkashe Mutane Da Sace Wasu Da Dama

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe mutane 3 a kananan hukumomin Giwa da Zangon Kataf a jiya Litinin. Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun bada rahoton harin da ?an ta’adda suka kai a kauyen Garawa, Doka da Unguwan Yaya duka a yankin Fatika a karamar hukumar Giwa inda suka kashe mutane 2 tare da sace wasu da yawa. Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya shaida cewa ?an ta’addan sun kai hari wurin shakatawa a kauyen Wawan Rafi a karamar hukumar Zangon…

Read More

Da ?umi-?umi: Boko Haram Ta ?wace ?aramar Hukumar Guzamala Jihar Borno

Kakakin majalisar Jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawal ya bayyana cewa Boko Haram ce ke rike da gaba dayan karamar hukumar Guzamala a jihar. Ya musanta ikirarin ministan yada labarai, Lai Muhammad da kuma tsohon shugaban hedikwatar tsaro, Maj Gen Gabriel Olonisakin da suka ce an kwace gaba dayan kananan hukumomin jihar daga hannun Boko Haram. Kakakin majalisar, yace daga karamar hukumar Guzamala ya fito kuma gaba dayan karamar hukumar har yanzu tana hannun Boko Haram ne. Ya bayyana hakane yayin ganawa tsakanin kungiyar wanda suka fito daga karamar hukumar ta…

Read More

Matsalar Tsaro: Dr. Gumi Na Cigaba Da Ganawa Da Fulani

Cikin alkawarin da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi lokacin da ya tattauna da fulanin dajin Jere a ranar 3/1/2021 domin kawo karshen rashin zaman lafiya da kidnapping da kashe-kashe a hanyar Abuja. Na samar musu da makaranta da Asibiti da wurin kiwon shanu. Yau Allah ya azurta Malam da daura harsashin wannan gini kuma yayi masa lakabi da Sheikh Usman bn Fodio Center (Kagarko Grazing Reserve). In da za a gina musu makaranta da asibiti da wurin da zasu rika shayar da dabbobinsu. Kafin shigarsa dajin sai da ya tsaya…

Read More

Shugaban ‘Yan Sanda Zai Yi Murabus

A yau Litinin ne ake sa ran cewa babban Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, da dumbin wasu manyan jami’ai zasu yi ritaya daga aiki. Shugaban ‘yan Sandan Mohammed Adamu da sauran manyan jami’an zasu yi ritaya ne saboda sun ?arewar wa’adin lokacinsu na aiki, kamar yadda doka ta tanada. Adamu, wanda ya shiga aikin dan sanda a ranar 1 ga watan Fabarairu na shekarar 1986, zai yi ritaya sakamakon cika shekaru 35 yana aiki. A watan Janairu na shekarar 2019 tsohon shugaban ‘yan Sanda Ibrahim Idris ya mika…

Read More

A Haramta Shigar Da Shanu Kudancin Najeriya – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya dace a saka dokar da za ta hana kai shanu daga arewa zuwa kudu, domin da?ile rikicin da ya ?i ci ya ?i cinyewa tsakanin Manoma da Makiyaya a ?asar. A yayin zantawa da manema labarai bayan haduwarsa da gwamnonin APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina, Ganduje ya ce idan har ba a hana yawon shanu ba, babu ranar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya. Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta shirya samar da wurin zama ga…

Read More

Shugaban Kasa Ya Canza Dogari

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya canza dogarinsa mai kula da tsaronshi wanda akafi sani da ADC, kuma ya zabi sabon Dogarin da zai cigaba da kula da tsaronshi nan take. Fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa Laftanan Kanal Y. M Dodo zai maye Kanal Muhammed Abubakar, wanda ya ke matsayin Dogarin Buhari tun 2015. A cewar majiyoyin, Kanal Abubakar zai ajiye aikinsa ne saboda halartan wani kwas domin ya samu karin girma zuwa matsayin Birgediya Janar. Laftanan Kanal Dodo ya kasance hadimi ga kwamandan makarantar Sojoji NDA dake Kaduna.…

Read More

Ba Za Mu Lamunci Zaman Sarkin Fulani A Oyo Ba – Yarbawa

Al’ummar Yarbawa Mazauna Garin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar Oyo sun dauki alkawarin cewa ba za su sake barin sarkin Fulani da aka kora a garin, Abdulkadri Saliu, ya sake dawowa ba har abada. A cewarsu, barin shi ya sake dawowa garin daidai ya ke da kashe kansu da kansu, sun kara da cewa gara su mutu da su amince Saliu ya dawo garin. “Gara dukkan garin su kashe kansu a maimakon su bari Sarkin Fulani ya dawo. Gara mu sadaukar da rayukan mu a…

Read More

Sokoto: ?an Majalisa Ya Harbe ?an Bindiga

?an majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a majalisar wakilai, Abdullahi Salame ya bindige wani dan fashi har lahira, yayin da ya rauna ta abokansa a lokacin da suka je gidan shi da ke unguwar Bado a Sokoto da karfe ukun dare don yi masa fashi. Dan majalisar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sokoto tare da sa hotunan yadda lamarin ya kasance a shafinsa na sada zumunta. Cikin abubuwan da ya nunawa duniya a shafin sa na sada zumunta sun hada da hula,(face cap) da…

Read More

Sokoto: ?an Majalisa Ya Harbe ?an y

?an majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a majalisar wakilai, Abdullahi Salame ya bindige wani dan fashi har lahira, yayin da ya rauna ta abokansa a lokacin da suka je gidan shi da ke unguwar Bado a Sokoto da karfe ukun dare don yi masa fashi. Dan majalisar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sokoto tare da sa hotunan yadda lamarin ya kasance a shafinsa na sada zumunta. Cikin abubuwan da ya nunawa duniya a shafin sa na sada zumunta sun hada da hula,(face cap) da…

Read More

Sokoto: ?an Majalisa Ya Harbe ?an Fashi

?an majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a majalisar wakilai, Abdullahi Salame ya bindige wani dan fashi har lahira, yayin da ya rauna ta abokansa a lokacin da suka je gidan shi da ke unguwar Bado a Sokoto da karfe ukun dare don yi masa fashi. Dan majalisar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sokoto tare da sa hotunan yadda lamarin ya kasance a shafinsa na sada zumunta. Cikin abubuwan da ya nunawa duniya a shafin sa na sada zumunta sun hada da hula,(face cap) da…

Read More

Na Yi Murnar Sallamar Shugabannin Tsaro – Shettima

Sanata mai wakiltar Maza?ar Borno ta tsakiya Sanata Kashim Shettima daga jam’iyyar mai mulki ta APC, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya zabo mutanen da suka cancanta yayin nadin sabbin manyan hafsoshin sojoji na kasar da aka yi kwanan nan. Shettima ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin da ‘yan jarida suka nemi jin ra’ayinsa game da nadin musamman da Buhari ya yi na sabbin shugabannin tsaro, duba da cewa makwanni da suka gabata ya yi kira ga shugaban kasar ya sauya shugabannin tsaron. Ya ?ara da cewar Buhari ya…

Read More

Korona Da Ta’addanci ?anjuma Ne Da ?anjummai – Buhari

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatar kasashen duniya su hada kai tare wajen tunkarar cutar COVID-19 kamar sauran kalubalen da suka ji?inci rashin tsaro da ke addabar duniya. Da yake jawabi a wajen taron karbar takardun wasikar amincewa da sabbin jakadun Masar, Saudi Arabia da Argentina a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana cewa:“Muna da kalubale iri daya da ke tasiri sosai ga kasashenmu, wadanda suka hada da ta’addanci, tayar da kayar baya, canjin yanayi, fashewar jama’a, safarar mutane, rashawa, talauci, da…

Read More

Buratai Ya Mi?a Ragamar Tsaro Ga Sabon Shugaban Dakarun Soji

A wannan taro mai kayatarwa da aka gudanar a farfajiyar taron hedkwatar sojin kasa dake birnin tarayya Abuja, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya mika tutan fara aiki ga sabon shugaban hafsan Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru. An yi taron mika mulki daga hannun wanda ya sauka daga karagar zuwa sabon da shugaban kasa ya nada, a ranar Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021. Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata…

Read More

Bauchi: An Dam?e Matasa Masu Addabar Jama’a

A ranar ashirin da bakwai 27 ga watan janairun nan ne, Jami’an tsaro na Yan’sanda masu bin kwakwaf wadan ake kira Rapid Response Squard (RRS) a turance suka Kai sumame ma wasu gungun matasa da suka Addabi mutane unguwan Abujan Kwata, Kofar Wambai da kuma wasu sassan Jihar da kwacen wayoyi da hallaka su. Kakakin rundunar Yan’sanda na Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, a madadin kwamishinan Yan’Sanda Lawan Tanko Jimeta ya fitar da sanarwar ga manema labarai, inda yace a dalilin sumamen sun sami nasarar chapke akalla matasa ashirin da…

Read More

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Umar Ra??a

Allah ya yi wa Alhaji Aminu Umar Radda rasuwa, sakamakon harbin da ‘yan bindiga suka yi masa a lokacin da suka je garin Radda, da ke karamar hukumar Charanchi, a jihar Katsina. Inda suka sace mai garin kuma yaya a gurin shi. Alhaji Aminu Umar Radda, wanda yaya ne ga Shugaban Hukumar Kula Da Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i Na Nijeriya wato (SMEDAN) Dr. Dikko Umar Radda (Gwagwaren Katsina) Majiyarmu ta tabbatar mata cewa bayan raunin da ya samu, aka kai shi wani asibiti a Kano, a can ya rasu. A…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Nemi Miliyoyin Ku?i Kafin Sakin Marayun Abuja

‘Yan bindigar da suka sace wasu marayu daga gidan da ake kula da su a babban birnin tarayya Abuja sun bukaci a biyan diyyar naira miliyan 10 akan kowanne maraya guda kafin sakinsa. ‘Yan bindigar sun kuma bukaci biyan naira miliyan goma kan mai gadin gidan da wani magidanci Momoh Jimoh da iyalinsa, da kuma wata mata Rukaiyat Salihu. Wata majiya a gidan marayun ta shaidawa Jaridar Daily Trust cewar, ‘yan bindigar sun buga waya a ranakun Lahadi da jiya Litinin domin neman diyyar. Wani dan uwan magidancin da aka…

Read More

An Sace Jami’ar Ya?a Labarai Ta Hukumar Shige Da Fice

Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami’a mai magana da yawun hukumar shige da fice ta kasa, reshen jihar Edo, Bridget Esene. Wani jami’in hukumar ya bayyana cewa an sace Mrs Esene ne ranar Lahadi a kan hanyarta ta zuwa coci. An bayyana cewa ‘yan bindigar sun ta bibiyar jami’ar ne Esene har zuwa yankin Igueniro, dake babban birnin jihar, inda suka fitar da ita daga motarta suka jefa ta a motarsu. Sha’anin satar mutane da yin garkuwa da su domin amsar ku?in fansa na cigaba da zama wani…

Read More

Tsaro Ya Samu A Mulkin Buhari Fiye Da Gwamnatocin Baya – Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa jami’an tsaro na aiki tukuru don kare rayukan ‘yan Nijeriya. Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja, Ministan ya kara da cewa, yanayin tsaron Nijeriya a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya fi na gwamnatocin da suka gabata inganci. Lai Mohammed ya kuma ya bayyana wasu nasarorin da jami’an tsaro suka samu yayin gudanar da ayyukansu. Ya ce: “Zan iya fada ba tare da jinkiri ba cewa, duk da cewa Najeriya na fuskantar kalubalen…

Read More

Kano: Da Tsohon Saurayina Na Fara Yin Garkuwa – Mai Garkuwa

Rundunar yan sandan Jihar Kano a ranar Laraba ta cafke wasu masu garkuwa da mutane su hudu cikin su har da mace yar shekara 23, Maryam Mohammed, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ta shaida cewa aikin ta na farko a matsayin mai garkuwa da mutane ya fara ta kan tsohon saurayin ta wanda yaki auren ta bayan shafe shekaru suna soyayya. Maryam Mohammed, wanda aka fi sani da Hajiya, an kama ta a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu mutane uku yan tawagar ta a unguwar Jaba,…

Read More

Kano: Da Tsohon Saurayina Na Fara Yin Garkuwa – Maryam

Rundunar yan sandan Jihar Kano a ranar Laraba ta cafke wasu masu garkuwa da mutane su hudu cikin su har da mace yar shekara 23, Maryam Mohammed, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ta shaida cewa aikin ta na farko a matsayin mai garkuwa da mutane ya fara ta kan tsohon saurayin ta wanda yaki auren ta bayan shafe shekaru suna soyayya. Maryam Mohammed, wanda aka fi sani da Hajiya, an kama ta a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu mutane uku yan tawagar ta a unguwar Jaba,…

Read More