Sanata mai wakiltar Maza?ar Borno ta tsakiya Sanata Kashim Shettima daga jam’iyyar mai mulki ta APC, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya zabo mutanen da suka cancanta yayin nadin sabbin manyan hafsoshin sojoji na kasar da aka yi kwanan nan.
Shettima ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin da ‘yan jarida suka nemi jin ra’ayinsa game da nadin musamman da Buhari ya yi na sabbin shugabannin tsaro, duba da cewa makwanni da suka gabata ya yi kira ga shugaban kasar ya sauya shugabannin tsaron.
Ya ?ara da cewar Buhari ya dauki lokacinsa domin gano kwamandojin sojoji da suka cacanta kuma suke da ilimi kan yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram duba da cewa dukkansu sunyi aiki a Borno a baya.
“Shugaban kasa ya yi zabi mai kyau. Na yi mu’amala da wasu daga cikinsu kuma na tabbatar da kwarewarsu da jajircewa.
Janar Leo Irabor na daga cikin kwararun babban hafsan tsaro da aka taba samu a Najeriya.
“Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Babban hafsan sojojin ruwa, ya yi aiki a Borno haka shima Janar Ibrahim Attahiru, Babban hafsan sojojin kasa ya yi aiki na kankanin lokaci,”
Tsohon gwamnan na Borno ya ce babu wata matsala tsakaninsa da tsaffin manyan hafsoshin sojojin sai dai ya yi kira a sauke su ne domin samun zaman lafiya a Borno da kasa baki daya.
