Zan Gyara Kwamacalar El Rufa’i Idan Na Zama Gwamna – Shehu Sani

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a za?en 2023.

Yayin hira da wani gidan rediyo a jihar, sanatan ya yi alkawarin wanke abun da ya kira ”tabargazar gwamnan jihar mai ci Nasir El-Rufa’i” idan ya yi nasara.

”Duk wanda ya musguna wa jama’a ya ?untata musu bai cancanci ya samu kowacce irin dama ba, domin duka addinanmu sun girmama ?an adam”.

Shehu Sani ya ?ara da cewa a yanzu ya rage wa jam’iyyar PDP ta ha?e kan ?a?anta don ?watar mulki a hannun APC.

Related posts

Leave a Comment