Da ?umi-?umi: Boko Haram Ta ?wace ?aramar Hukumar Guzamala Jihar Borno

Kakakin majalisar Jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawal ya bayyana cewa Boko Haram ce ke rike da gaba dayan karamar hukumar Guzamala a jihar.

Ya musanta ikirarin ministan yada labarai, Lai Muhammad da kuma tsohon shugaban hedikwatar tsaro, Maj Gen Gabriel Olonisakin da suka ce an kwace gaba dayan kananan hukumomin jihar daga hannun Boko Haram.

Kakakin majalisar, yace daga karamar hukumar Guzamala ya fito kuma gaba dayan karamar hukumar har yanzu tana hannun Boko Haram ne.

Ya bayyana hakane yayin ganawa tsakanin kungiyar wanda suka fito daga karamar hukumar ta Guzamala. A karshe yayi kira ga sabbin shuwagabannin tsaro da su taimaka wajan kwato karamar hukumar daga hannun Boko Haram dan kawo zaman lafiya a cikinta.

Related posts

Leave a Comment