Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar ‘Yan sanda a jihar sun cafke wata mai shekaru 30, mai suna Fatima Lawali dauke da harsashi na bindigar AK-47 har guda 991, akan hanyarta ta shiga dokar daji wurin ‘yan bindiga. Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba Elkanah, yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma’a ya bayyana hakan, ya ce wacce ake zargin tana kan hanya ne zuwa kai wa wani hatsabibin dan bindiga mai suna Ado Alero, wanda ya dade yana adabar mutanen Zamfara da kewaye…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda Zai Dagula Lissafi – Gumi
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ayyana yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda kawai mataki ne da aka dauka na siyasa, wanda babu abin da zai canza illa dagula lissafi. Malamin ya ?ara da cewar gwamnatin tarayya ta yarda wani sashi na kafafen watsa labarai a kasar suna juya ta yadda suka ga dama, yana mai cewa hakan ba zai kawo wani sauyi a kasa ba. “Ina tunanin gwamnatin tarayya ta bari kafafen watsa labarai na wani yanki…
Read MoreKaduna: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Matafiya Sun Nemi Miliyan 200
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun shaida wa iyalan ?an sandan da suka sace su tattara musu miliyan N200m domin a sako shi saboda zasu bar wurin da babu sabis. An ruwaito cewa Dan sandan mai suna Dambo Hosea, na ?aya daga cikin matafiyan da aka sace ranar Lahadi, a kan hanyar Kaduna-Abuja. Shine jami’in dan sandan dake tare da tsohon ?an takarar gwamnan Zamfara, wanda ?an bindiga suka kashe yayin harin. Tsagerun yan bindigan sun nemi iyalai su tattara musu zunzurutun kudi…
Read MoreBoko Haram Ne Ke Addabar Hanyar Kaduna Zuwa Abuja – Bincike
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Bincike ya bayyana cewa hare-haren da ake yawan kai wa babban titin Abuja zuwa Kaduna duk ‘yan Boko Haram ne suke kai farmakin. A ranar Lahadi, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da ba a san yawansu ba sannan sun halaka wani fitaccen dan siyasan jihar Zamfara, Sagir Hamidu a wani wuri mai suna Kurmin Kare a kan hanyar. ‘Yan ta’addan sun kara komawa kusa da wurin sannan suka kara budewa wasu matafiya wuta har suka yi garkuwa da…
Read MoreBoko Haram Sun Kafa Jamhuriya A Jihar Neja
Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa Boko Haram sun kafa sansanoni a cikin ?ananan Hukumomin Shiroro da kuma Borgu da ke cikin Jihar. Sai dai a wannan karon, Gwamnatin Jihar Neja ta ?ara fito da mummunan halin da ake ciki a yankunan, inda a cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Matane ya yi wa manema labarai ranar Talata a Minna, ya ce tuni har ‘yan ta’adda sun fara bi cikin Masallatan Juma’a su na wa’azi a ?auyuka cewa jama’a su…
Read More‘Yan Bindiga Sun Sake Tafka Mummunan Ta’asa A Katsina
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari ?auyen Barawa dake yankin karamar hukumar ?atagarawa ta jihar, inda suka yi mummunan ta’adi. Rahotanni sun bayyana cewa yayin harin na ranar Lahadi, maharan sun kashe a?alla mutun 4, tare da jikkata wasu da dama. Wani mazaunin ?auyen Barawa ya shaida wa manema labarai cewa yan bindigan sun farmaki kauyen ne a kan dandazon babura, kuma kowane ?auke da makami. Ya kuma kara da cewa yan bindigan sun kwashe fiye da mintuna 90…
Read MoreJiragen Yakin Soji Sun Yi Ruwan Bama-Bamai Kan ‘Yan Bindiga
Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wani ruwan bama-bamai da jirgin yakin rundunar Operation Hadarin Daji ya yi, ya hallaka adadi mai yawa na yan bindiga a yankin arewa ta yamma. A rahoton PRNigeria, harin jirgin yakin, wanda sojojin sama suka aiwatar a Dangwandi da Tsakai dake karamar hukumar Isa, ya yi sanadin mutuwar ?usoshin yan bindiga da dama. Kazalika makamancin irin wannan ruwan bama-baman ta sama, ya hallaka kayayyakin amfani yan bindiga da yawan gaske a wasu sassan Zamfara.
Read More‘Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya Masu Yawa A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dimbin matafiya daga cikin motocinsu a babbar hanyar Kaduna zzuwa Abuja da yammaci Lahadi, 21 ga Nuwamba, 2021. Har yanzu ba’a san adadin wadanda aka sace ba. Wani faifan bidiyo da aka saki a kafafen ra’ayi da sada zumunta ya nuna motoci akalla biyu da aka kwashe wadanda ke ciki a tsakiyar titi. A bidiyon mai da?i?a 31, an ji mai daukan bidiyon yana cewa: “Wayyo Allah, sun…
Read MoreDa Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Dan Takarar Gwamnan Zamfara
Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun kashe Sagir Hamidu, tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a shekarar 2019, a babban hanyar Abuja zuwa Kaduna. Marigayi dan siyasan ya nemi kujerar gwamnan ne a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin kasa. Maharan sun bindige shi har lahira ne yayin da suka bude wuta kan matafiya a kusa da Rijana misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi. Majiya daga jami’an tsaro da suka nemi a boye sunansu sun tabbatar wa da mutuwarsa…
Read MoreNeja: Gwamnati Ta Haramta Cinikin Babura
Labarin dake shigo mana daga Minna Babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello ta haramta siyar da babura a cikin jihar. Babban sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, wanda ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Asabar, ya ce hukuncin ya biyo bayan matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a wasu yankunan jihar. Ya kuma ce an dauki matakin ne saboda bukatar da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke gabatarwa na neman a basu babura…
Read MoreBorno: Zulum Ya Yi Wa ‘Yan Gudun Hijira Sha Tara Ta Arziki
Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da tsabar kudi har sama da rabin biliyan daya. ‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri. A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin…
Read MoreAn Yi Nasarar Dakushe Karfin ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina
Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnatin jihar a ranar Alhamis tace yan bindiga sun kashe mutum 213, sun sace 676 a fa?in kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, jihar a fa?in Jihar. Gwamnatin jihar na cewa yan bindigan sun aikata wannan ta’adi ne tsakanin watan Yuli zuwa Octoba, 2021. Gwamnatin ta kara da cewa a wannan tsawon lokacin jami’an tsaro sun samu nasarar damke mutum 724 da ake zargi da aikata ta’addanci kan mutane a jihar. Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, shine ya bayyana…
Read MoreZulum Ya Bada Tallafin Miliyan 20 Ga Iyalan Marigayi Janar Dzarma
Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya jagoranci tawaga zuwa ta’aziyyar marigayi Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, wanda ‘yan ta’addan ISWAP suka kashe kwanaki a jihar Borno. Gwamnan ya gana da iyalan marigayin a sansanin soji na Ribadu dake jihar Kaduna, kuma nan take ya bada umarnin sakin miliyan 20 ga iyalan don tallafa musu. A wata sanarwa da ofishin gwamna Zulum ya fitar a dandalin Facebook, Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, yace nan take aka tura musu kudin. Gusau ya ?ara da…
Read MoreAdamawa: An Ceto Uwa Da ‘Yarta Daga Hannun ‘Yan Bindiga
Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Rundunar ‘yan Sandan jihar tayi nasaran ceto wata uwa ma shayarwa wadda akayi garkuwa da ita tare da ‘yarta ‘yar shekaru biyu da haihuwa. Kakakin rundunan ‘yan Sandan jihar DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a birnin Yola. DSP Suleiman Yahaya yace ofishin Rundunar dake karamar hukumar Gombi a jahar Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta ne aka samu nasaran ceto matar mai suna Jimrewa Las.…
Read MoreSaura Kiris Mu Ga Bayan ‘Yan Ta’adda A Najeriya – Rundunar Soji
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hafsan rundunar sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, ya tabbatar wa yan majalisar dattawa cewa lokaci ka?an ya rage ayyukan ta’addanci da yan bindiga ya zama tarihi a Najeriya. Amao ya bada wannan tabbacin ne kwanaki uku kacal bayan mayakan ISWAP sun kashe Janar na sojojin ?asa a Askira Uba, jihar Borno. Majalisar dattijai, ta hannun kwamitin sojojin sama, sun bukaci rundunar sojin su ?ara ?aimi a yakin da suke domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren da lamarin ya shafa. Hafsan…
Read MoreBabu Inda Nace Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda Zai Tarwatsa Najeriya – Gumi
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yace ana jingina masa maganganun da bai yi ba, ta hanyar ?age da sharri akan ‘yan Bindiga domin kawai a ?ata mishi suna. Shehin malamin ya musanta maganar da ake jingina masa cewa wai ayyana yan bindiga a matsayin yan bindiga zai kawo karshen Najeriya. Malamin ya bayyana cewa sam bai fa?i haka ba, mutane ne ba su fahimnci abinda yake nufi ba. Gumi ya fa?i haka ne yayin da yake…
Read MoreMafarauta Za Su Iya Dakile Matsalar Tsaro A Najeriya – Yahaya Bello
Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya roki yan majalisun tarayya su gaggauta amincewa da kudirin mafarauta 2020 ya zama doka, domin ganin bayan matsalar tsaro a Najeriya. Kudirin wanda ya tsallake karatu na ?aya da na biyu a dukka majlisun tarayya biyu, sanata mai wakiltar Ekiti ta kudu, Biodun Olujimi, shine ya gabatar da shi. Gwamna Bello ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin ?ungiyar mafarauta ta Najeriya a Abuja ranar Asabar, Bello yace mafarauta zasu taka…
Read MoreJama’ar Gari Sun Kwaci Sarkin Noman Kano Daga Hannun ‘Yan Bindiga
?aruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke wajen birnin Kano su ka ?waci wani shugabansu, Alhaji Yusuf Nadabo, mai shekara 80. Shi dai Nadabo shine mai gidan man Chiromawa Petroleum Station, sannan shine Sarkin Noman Kano. DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu bayanan cewa su dai ?an ta’addan, wa?anda su ka zo da muggan makamai domin yin garkuwa da Nadabo, sun dira a ofishin sa ne da ke Bakin Tasha da misalin ?arfe 7:35, in da su ka ri?a harbi sama domin su razana jama’a. Ai kuwa harbin nan na…
Read MoreBorno: ISWAP Sun Harbe Babban Janar Na Soja
Rahotanni daga Birnin Maiduguri na Jihar Borno, na bayyana cewar an harbe wani babban jami’in soja mai matsayin Birgediya Janar Dzarma Zirkushi har lahira yayin da maya?an rundunar dakarun ?asashen yankin tafkin Chadi, ISWAP, ta yi wa sojoji kwantan ?auna a jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa bayan Birgediya Janar ?in, akwai ?arin sojoji guda hu?u da su ma suka rasa rayukansu a kwantan ?aunar da ya auku a Bulguma, kilomitoci ka?an daga garin Askira na ?aramar hukumar Askira Uba. Rahotannin sun ?ara da cewa tuni aka tura dakarun 28…
Read More‘Yan Bindiga Sun Kakaba Wa Sakkwatawa Haraji
Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar kimanin wata guda bayan karbar naira miliyan 11 a matsayin kudin fansa domin sakin mutane 20 da suka yi garkuwa da su a garin Gatawa, ‘yan bindiga sun sake dawowa garin a ranar Laraba. A wannan karon, maharan sun sake sace mutane biyar, inda suka nemi a biya N500,000 a matsayin kudin fansarsu, kamar yadda majiyoyi suka bayyana a garin. A baya garin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto na daya daga cikin garuruwan da basu…
Read More