Jama’ar Gari Sun Kwaci Sarkin Noman Kano Daga Hannun ‘Yan Bindiga

?aruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke wajen birnin Kano su ka ?waci wani shugabansu, Alhaji Yusuf Nadabo, mai shekara 80.

Shi dai Nadabo shine mai gidan man Chiromawa Petroleum Station, sannan shine Sarkin Noman Kano.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu bayanan cewa su dai ?an ta’addan, wa?anda su ka zo da muggan makamai domin yin garkuwa da Nadabo, sun dira a ofishin sa ne da ke Bakin Tasha da misalin ?arfe 7:35, in da su ka ri?a harbi sama domin su razana jama’a.

Ai kuwa harbin nan na su bai razana al’umma ba, inda su ka tunkari ?an ta’addan, har ma wani a cikin jama’ar garin ya samu raunuka na harsashi, kamar yadda wata majiya ta shaidawa wannan jarida.

“?an ta’addan ba su samu nasara ba sabo da sun zo ne a ranar kasuwa. Akwai jama’a da dama ana ta hada-hada a yankin,” in ji shaidun gani da ido.

“Da su ka yi garkuwa da shi da ?an sa Isyaku. Sai su ka yi tattaki zuwa ma?abarta inda su ka ?oye baburan su. Amma ina, ai kuwa sai mutanen ?auyen nan su ka dake, su ka bi su suna Kabbara.

“Bayan da harsashin ?an ta’addan ya ?are, shima kuma Alhaji Nadabo ba zai iya ci gaba da tafiya ba sabo da tsufa, sai su ka kwashe illahirin ku?a?en da ke aljihunsa, kimanin dubu 80, sai su ka ranta a na kare,” in ji majiyar.

Mai magana da yawun rundunar ?an Sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, in da ya ?ara da cewa sun ku?utar da Sarkin Noman ta ha?in gwiwa da al’ummar garin da kuma ?an ?ato da gora na yankin.

“Mu na samun rahoton mu ka yi gaggawar tura jami’an mu wajen a daidai ?arfe 7:57. Da ha?in gwiwar al’umma da ?an ?ato da gora mu ka samu nasarar ku?utar da Sarkin. Mu ka kuma da?ile yun?urin yin garkuwa da shi,” in ji Kiyawa.

Related posts

Leave a Comment