Rahotanni daga Birnin Maiduguri na Jihar Borno, na bayyana cewar an harbe wani babban jami’in soja mai matsayin Birgediya Janar Dzarma Zirkushi har lahira yayin da maya?an rundunar dakarun ?asashen yankin tafkin Chadi, ISWAP, ta yi wa sojoji kwantan ?auna a jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan Birgediya Janar ?in, akwai ?arin sojoji guda hu?u da su ma suka rasa rayukansu a kwantan ?aunar da ya auku a Bulguma, kilomitoci ka?an daga garin Askira na ?aramar hukumar Askira Uba.
Rahotannin sun ?ara da cewa tuni aka tura dakarun 28 Task Force Brigade da ke Chibok domin ?arfafa tsaro a Askira, wanda ake kai farmaki.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoton yadda maya?an ISWAP suka dirar wa garin cikin jerin gwanon manyan motoci masu ?auke da bindigogi.
Wani ?an sintiri ya bayyana cewa maya?an sun durfafi wani sansanin soji inda suka fara musayar wuta da sojojin.
An yi wa sojojin kwantan ?auna a sa’ilin da suke kan hanyar kai wa sojojin da ke ?auki-ba-da?i da ‘yan tada ?ayar bayan ?auki.
“Yau ranar ba?in ciki ce a gurinmu a filin daga; mun rasa Birgediya Janar. Maya?an ISWAP sun yi wa Birgediya Janar ?in da sauran sojojin da ke kan hanyarsu ta kai wa sojojinmu da ke Askira ?arin ?arfi kwantan ?auna inda kuma suka harbe su har lahira. Muna cikin ?acin rai,” wata majiya ta tsaro ta fa?a.
Majiyar ta ?ara da fa?in cewa jiragen ya?i sun yi ruwan bamabamai a kan ‘yan ?ungiyoyin tada ?ayar bayan.
