Zunubban El Rufa’i Za Su Sa Mu Shiga Yajin Aikin Kasa Gaba ?aya – ?ungiyar Kwadago

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyar ?wadugo ta ?asa, NLC, ta aikewa Buhari wasi?a akan rashin aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da ?ungiyar ta sanyawa hannu tare da gwamnatin Kaduna, kan matsalar korar Ma’aikata da cin zarafin jama’ar Jihar.

Kwafin wasi?ar da aka aikewa Kamfanin dillancin labarai na ?asa NAN, ya nuna cewa shugaban kungiyar Kwadagon Ayuba Waba, ya sanya hannu a kan wasi?ar.

Wani ?angaren wasi?ar yace: “Ranka ya da?e, idan zaka iya tuna wa, mun yi taron sulhu na farko tsakanin NLC da gwamnatin jihar Kaduna a ranar 20 ga watan Mayu 2021.”

?ungiyar ?wadagon da gwamnatin jihar Kaduna sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a taron, wadda ta ?unshi cewa, gwamnatin ba zata sake ta?a ma’aikata ko yan kasuwa a jihar ba musamman wa?anda suka fito muka yi zanga-zanga tare.”

“Amma abun mamaki, bayan amincewa da wannan, gwamnatin Kaduna tayi fatali da dukkan wannan yarjejeniya da aka cimma wa tsakaninta da ma’aikata.” Mr. Wabba ya cigaba da cewa matu?ar gwamnatin Kaduna ta cigaba da cin zarafin ma’aikata, kuma ta?i aiwatar da yarjejeniyar da ta sanya wa hannu to zasu ?auki mataki.

Yace majalisar ?oli ta ?ungiyar NLC ta cimma matsaya cewa idan gwamnatin Kaduna ta tsaya kan bakarta na ya?i da NLC, to zata sake sabunta yajin aikin data janye a jihar, sannan zata yi kira ga ma’aikatan Najeriya baki ?aya su shiga yajin aiki.

Related posts

Leave a Comment