Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan tafiyarsa zuwa Belgium inda ya hallarci taron hadin kai na gamayyar kasashen Turai da gamayar kasashen Afrika karo na shida.
Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari na ya?a labarai gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ne ya sanar da labarin dawowarsa a shafinsa na Facebook.
Buhari Sallau, a cikin rubutun da ya wallafa a da yammacin jiya ya ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan nasarar halartan taron hadin kasashen Afrika da na Turai a Brussels.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa goron gayyatar da shugaban kasar jamhuriyyar Czech, Milos Zeman, na ziyartar kasar Turan a wannan shekara ta 2022. Wannan ya faru ne a zaman diflomasiyyar da ya gudana tsakanin Buhari da Milos Zeman ranar Alhamis a Brussels, kasar Beljika.
